Kamfanin dillancin labaran Faransa ya jiyo komishinan ‘yan sandan jihar ta Borno Aderemi Opadokun, na cewa harin ya yi muni matuka, kuma akwai yiyuwar adadin mamatan zai iya karuwa sakamakon munanan raunukan da suka sama.
Kwana daya kafin nan dai wasu da aka ce magoya bayan ‘yan Boko Haram ne sun harba manyan rokoki da suka fada a wasu unguwanni da ke gefen birnin na Maiduguri tare da kashe mutane akalla 8, kuma lamarin na faruwa ne a daidai lokacin da sabon shugaban kasar Muhammadu Buhari ya yi alkawalin mayar da babbar cibiyar gudanarwa ta aikin soja zuwa Maiduguri fadar gwamnatin Borno, domin kara daura damara wajen fada da mayakan wannan kungiya.ABNA